Help & User Manual

Do you want to get the most out of BIG Launcher? Are you stuck in the Preferences? Then this page is for you!

BIG Launcher User Manual

Read the User Manual online (English only) Download the User Manual as PDF file

FAQ - Tambayoyin da aka fi yi


Ya ake saka BIG Launcher a matsayin launcher ta ainihi?

Idan ka danna Madannin gida bayan ka saka application ɗin, za’a tambaye ka da ka zaɓi launcher ta ainihi daka duka launcher da akwai. Ka tabbatar ka zaɓi zaɓin ‘ Yi amfani da a na ainihi’ ko na ‘Ko yaushe’. Idan menu ɗin ya ƙi budewa, sai ka yishi da kanka - danna Madannin menu, tafi zuwa Saitin tsari >> Applications >> Applications na ainihi >> Nunin gida sai ka zaɓi ‘BIG Launcher’.

Tya zan mayar da tsohuwar launcher ta ta baya?

Zaka iya sake saita ainihin saitin launcher a wajan saituttuka. Idan wannan yaƙi yi, danna Madannin menu, tafi zuwa Saitin tsari >> Applications >> Applications na ainihi >> Nunin gida.

Na siya BIG Launcher a lokacin baya amma yanzu na kyauta kawai nike da. Taya zan dawo da lasisi na?

Turo muna lambar odar ka (daga receipt ɗin da muka turo maka a imel yayin da ka siya) da kuma adireshin ka na imel da kayi amfani da wajan siya mukuma zamu taimake ka dawowa da lasisin ka kyauta ma duka applications ɗin BIG Apps Suite.

Mai yasa aka raba BIG Launcher zuwa kashi guda 3?

Ranan 9 ga watan Maris, 2019, akwai wata ƙa'idar izini da akayi wadda ta shafi duka applications ɗin Google Play Store. Tun lokacin, BIG Launcher ta kasa iya samun damar shiga saƙonni da kiraye-kirayen waya ba, dan an bada damar wannan wanna izinin kawai ga applications masu amfani dashi a matsayin aikin suna ainihi kawai - ba launcher ba. Don bin wannan ƙa'idar, an cire wasu abubuwa daga application ɗin BIG Launcher sai aka saka su a applications daban-daban -  BIG Phone da BIG SMS. Saika ɗauko kuma ka saka su daban-daban.

Taya zan saka nuni da yawa a BIG Launcher?

Zaka iya saka nuni da yawa a cikin menu ɗin saituttuka. Saika haɗa sabbin nunin da ka haɗa tare da madannin da akwai, in ba haka ba, baza ka iya samun damar su ba. Ko kuma zaka iya kashe zaɓin motsa yatsa tsakanin su nunin a cikin menu ɗin  saituttuka. Don Allah karanta jagorar mai amfani don ƙarin bayanai.

Taya zan goge abubuwan saƙo/lamba/rajistan ayyukan kira?

Saboda dalilan tsaro, gogewa na a kashe ainihi. Zaka iya kunna gogewar abubuwa a sashin su na saituttuka. Don Allah karanta jagorar mai amfani don ƙarin bayanai.

Babu ƙarar ringi a kira mai shigowa.

Tafi zuwa saituttuka >> Waya sai ka kunna zaɓin “Gyara: babu sautin ringi”. Idan wannan bai taimaka ba, yi muna rubutu a contact@biglauncher.com.

Saƙonni basu shigowa gabaɗaya.

Tafi zuwa saituttuka >> Saƙonni sai ka kunna zaɓin  “Gyara: wani zaɓin abun karɓan saƙo”.  Idan wannan bai taimaka ba, yi muna rubutu a contact@biglauncher.com.

Yadda ake kunna madanni masu ƙibtawa ma wasu application kaman Whatsapp, Gmail, Facebook Messanger, da sauran su.?

Idan aka kunna, duk wani application na wani kamfani daban zai haɗa sanarwa kuma zaka samu gajriyay hanyar samun wannan application ɗin a tattare da wani daga cikin madannin BIG Launcher, zai ƙibta har sai ka kunna application ɗin. Don kunna wannan halin, tafi zuwa saituttuka >> Zaɓuɓɓukan sikrin sai ka kunna zaɓin “Madanni mai ƙibtawa yayin da application ya nuna sanarwa”. A cikin nuni na gaba, kunna damar sanarwa na BIG Launcher

Taya ake kunnawa ko kashewar ƙarar sanarwar saƙo?

Tafi zuwa Saitin tsari >> Applications. Nemi application ɗin “BIG SMS na manya”, saka shi kuma ka zaɓi “Sanarwa” a nuni na gaba.

Taya ake saka ƙararrawa?

Taɓa agogo ko kwanan wata a nunin gida. Idan aka saita wani ƙararrawa, ana nuna gunkin ƙararrawa a gaba agogo. Zaka iya saka wani application ɗin alarm na daban a cikin editan madannin BIG Launcher

Menene iyakar BIG Apps Suite na kyauta?

Iyakar BIG Launcher na kyauta
- zaka iya gyara jerin hannun daman madanni kawai
- ƙarin nuni guda 5 kawai aka bari
- kariyar kalmar sirri na satuttuka ba zai yiwu ba
- nunu mai tunatar da kai akan siyan cikaakken na nunanwa lokaci zuwa lokaci


Iyakar BIG Phone na kyauta
- mafi sababbin abubuwa guda 5 a rajistan ayyukan kira kawai suke a bayyane
- wajan danna lambobi na a kashe yayin kiran


Iyakar BIG SMS na kyauta
- mafi sababbin saƙonni guda 5 kawai suke a bayyane
- bayan aika saƙonni guda 20, ana saka rubutu mai tare da haɗi zuwa biglauncher.com a kowane saƙo


See the version history here: BIG Launcher changelog

Josh, 27: "I’m tired of trying all those launchers, they all look the same. BIG Launcher is something completely different. And it is very effective."
John, 49: "50% of people over 40 years old suffer from hyperopia and they need glasses for reading. BIG Launcher is a great and simple solution for their problem."